
Hadimin shugaban kasa, me bashi shawara akan harkar jama’a, Aliyu Audu ya ajiye aikinsa na baiwa shugaban kasar ahawara.
Ya bayyana hakane a sakon da ya aikawa shugaban kasar a cikin wasika ranar 8 ga watan Yuni inda yace yana godiya matuka da damar da shugaban kasar ya bashi na bautawa kasarsa.
Ya yabawa tsohon hadimin shugaban kasar, Ajuri Ngilale wanda yace ta sanadiyyarsa ne ya samu wannan mukami.
Shima dai Ajuri Ngilale ajiye mukaminsa yayi daga Gwamnatin Tinubu.
Hakanan bayanshi, akwai Hakeem Baba Ahmad da shima ya ajiye mukamin nasa.