Sunday, November 16
Shadow

Duk da karin kudin wutar Lantarki da kamfanonin wutar Najeriya suka yi, aun tafka Asara

Kamfanonin rarraba wutar Lantarki na Najeriya Discos sun bayyana cewa, sun tafka asarar Naira Biliyan N202bn a watanni 3 na farkon shekarar 2025.

Hakan na zuwane duk da kara kudin wutar da kamfanonin Discos din suka yi.

Rahoton yace an yi karin kudin wutar da kaso 106.68 cikin 100.

Rahoton yace kamfanonin wutar Lantarkin da ake dasu guda 12 sun aikawa da mutane bill din wuta na Naira Biliyan N761.91bn a tsakanin watan Janairu zuwa Maris.

Saidai naira Biliyan N559.3bn ce kwastomomin suka iya biya a matsayin kudin wutar.

Hakan na nufin ba’a biya Naira Biliyan N202.61bn na kudin wutar.

Idan aka kwatanta da shekarar 2024, inda kamfanonin wutar suka aikawa kwastomomin bill din Naira Biliyan N368.65bn amma suka karbi Naira Biliyan N291.62bn, basu karbi Naira Biliyan N77.03bn ba, ana iya cewa kamfanonin wutar Lantarkin sun samu ci gaba.

Karanta Wannan  Ɓangarori uku da Saudiyya ta yi alƙawarin taimaka wa Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *