
Uwargidan marigayi tsohon shugaban Najeriya, Maryam Abacha, ta musanta zargin da ake yi wa mijinta, tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar Sani Abacha, kan zargin satar kuɗin Najeriya.
Abacha ya yi mulkin Najeriya ne daga shekarar 1993 zuwa 1998 kuma ya rasu ne a ranar 8 ga Yunin 1998.
DailyTrust ta rawaito a cikin wata hira da gidan talabijin ɗin TVC ya yi ta yi a ranar Lahadi kan cikar Abacha shekaru 27 da rasuwa, uwargidan marigayin ta ce kuɗin da ake zargin mijinta ya sata, ba satar su ya yi ba, kawai ana yi masa mummunar fassara ce.
A cikin waɗannan shekarun baya-bayan nan, gwamnatoci daban-daban sun sanar da gano miliyoyin kuɗin dalar Amurka a asusan ƙasashen waje waɗanda ake wa laƙabi da “Abacha loot.”
Waɗannan kuɗaɗe, an dawo da su daga ƙasashen Switzerland da Amurka da Ingila da kuma ake amfani da su wajen ba da tallafi.
A yayin gabatar da hirar, Maryam ta ce waɗanda suka yin wannan zargi ba su da wata hujja.
“Wane ne zai ba da shaida kan cewa sace waɗannan kuɗaɗe aka yi?”
“Shin ka ga wata hujja game da kuɗin da aka kai wajen? Kuma kuɗin da mijina ya ajiye wa Najeriya, a cikin ‘yan watanni, an nemi kuɗin an rasa. Amma mutane ba sa magana a kan haka,” ta faɗa.
Ta ce yawan nuna mijinta da yatsa da ake yi na nuna akwai matsala a cikin al’ummarmu.
“Me ya sa kuke zargin mutum? Shin wannan ƙabilanci ne ko ƙyama ce ta addini? Meye matsalar ‘yan Najeriya ne?” ta tambaya.
“Ina yi wa ‘yan Najeriya addu’a. Ina yi mana gabaɗaya addu’a. Ina addu’ar Allah ya nufe mu da samun kyakkyawar zuciya. Mu daina yin ƙarya da zargin mutane.”
”Me ya sa muke nuna mummunan hali ga junanmu? Saboda kawai mutum ɗan Arewa ne ko kuma ɗan Kudu ko kuwa saboda mutum Musulmi ne ko Kirista ne, wannan ba daidai ba ne, kuma ba adalci ba ne.”
Maryam ta kuma caccaki ‘yan Najeriya da suke yarda da gwamnatocin da suka biyo baya da ke cewa sun gano wasu kuɗi da Abacha ya ɓoye a ƙasashen waje.
Ta ce, “Saboda ‘yan Najeriya shashashu ne kuma suke sauraron irin wancan batun.”
“Babangida ba shi ne Najeriya ba. Abacha ba shi ne Najeriya ba. Abiola da kowa da kowa, ba wanda shi ne zai kira kansa Najeriya. Dukkaninmu muna da muhimmanci.
“Kowane mutum ɗaya da ke yawo a titi yana da muhimmanci. Dukkaninmu mutane ne. Duk wannan sa-toka-sa-katsin a daina shi haka. Babangida bai isa ya sa ko kar ya sa abu ya faru ba.”
Sannan ta yi watsi da iƙirarin da ake cewa Abacha ne ya jagoranci soke zaɓen ranar 12 ga watan Yunin a lokacin mulkin Babangida.
“Abin da na sani game da soke zaɓen shi ne ba mijina ne ya yi ba,” in ji Maryam.
“Idan shi ne ya yi, hakan ya nuna ashe yana da ƙarfin iko…ƙarfin iko sama da na shugaban ƙasa. Idan har shugaban ƙasa na nan, amma wani ne ke zartar da abin da zai faru, kenan hakan na nufin Abacha ne a saman kowa.”