
Tsohon shugaban sojojin Najeriya, Janar Yusuf Tukur Burataiya musanta rahoton dake cewa an kai masa hari ya sha da kyar.
A baya dai an ruwaito Sanata Ali Ndume yana cewa An kaiwa Buratai hari, saidai daga baya yace yana nufin garin Buratai ne ba tsohon shugaban sojojin ba.
Buratai a sanarwar da ya fitar yace a Abuja yayi bikin Sallah tare da iyalinsa da ‘yan uwa da abokan arziki.
Yace maganar an kai masa hari bata da tushe ballantana makama inda yace ayi watsi da labarin.
Yace yana godiya ga wadanda suka kirashi dan jin halin da yake ciki bayan samun wannan labari.