RASHIN TAUSAYI:Ana zargin an sace wayar Adam A. Zango bayan ya yi haɗarin Mota.

Wasu rahotanni sun nuna cewa Fitaccen Jarumin Kannywood Adam A. Zango ya rasa ɗaya daga cikin wayoyinsa ƙirar (Samsung) tare da kuɗi, biyo bayan sun samu haɗarin Mota a hanyar Kaduna zuwa Kano.
Haɗarin wanda ya faru a ranar Lahadi, wanda tuni jarumin ya samu kulawa daga likitoci.
Hakanan hadda cincin din da mahaifiyarsa ta bashi an sace.
Wasu rahotanni sun ce Ali Nuhu ne ya dauki nauyin hidima da Adam A. Zango bayan hadarin motar.