
Jigo a jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi ya bayyana cewa, a Shirye yake ya koma jam’iyyar APC duk da a baya ya soki jam’iyyar da salon mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.
Yace lallai a baya ya soki Gwamnatin Tinubu amma a yanzu idan dai ya samu dama, zai iya komawa jam’iyyar APC.
Yace kuma a shirye yake dan yin aiki tare da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu din domin ko da a baya dama yayi aiki tare dashi.