
Wani me fana aji a yankin yarbawa wanda kuma dan PDP ne ne suna Segun Sowunmi ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yafi Atiku Abubakar da Peter Obi wayau.
Segun Sowunmi tsohon me magana da yawun Atiku ne wanda yace haduwarsa da Tinubu ba tana nufin ya ci Amanar Atiku bane.
Yace a matsayinsa na mutum me hankali yana da ‘yancin yin abinda yake so.
Ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels TV duk da yake cewa a baya ya soki gwamnatin Tinubu sosai.