Friday, December 5
Shadow

Ba dan kin goyon bayan Atiku da muka yi ba da yanzu ya jefa kasar cikin wahala da rikici>>Inji Wike

Ministan babban Birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa ba dan kin goyon bayan Atiku Abubakar da suka yi ba shi da gwamnoni da suka kira kansu da G5 ba da Tuni kasarnan na cikin rikici.

Wike da sauran gwamnonin da suka hada dana Seyi Makinde na jihar Oyo da Samuel Ortom na jihar Benue, da Okezie Ikpeazu na jihar Abia da Ifeanyi Uguanyi na jihar Enugu ne suka hadewa Atiku kai.

Sun ce ba zasu goyi bayan Atiku ba inda suka goyi bayan Tinubu wanda hakan na daga cikin dalilin da yasa Atiku Abubakar ya fadi zabe.

Wike a wajan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP ya bayyana cewa, ba su yi nadamar abinda suka aikata ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda aka kama wasu masu Gàrkùwà da mutane aka musu tsìràrà ana duka kamar jakai

Yace duk da rikicin dake cikin PDP, jam’iyyar ba zata ruguje ba.

Ya bayyana cewa a ko da yaushe bin dokar jam’iyya da na kundin tsarin mulkin Najeriya na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *