Friday, December 5
Shadow

Masu zaben Tinubu su je su zabeshi mu dai ba zamu zabeshi ba saboda bai tsinana mana tsiyar komai ba>>Inji Inyamurai

Inyamurai sun bayyana cewa, Ba zasu zabi shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben shekarar 2027 me zuwa ba.

Sun bayyana cewa saboda shugaban bai yiwa yankunsu na kudu maso Gabas wani abin a zo a gani ba.

Dattawan Inyamuran sun ce idan aka tafi a haka Tinubu ko kaso 25 din da ake samu ba zai samu ba a yankin nasu.

Jagoran dattawan, Prof. Charles Nwekeaku ne ya bayyana hakan inda yace Tinubu bai yi abinda zasu zabeshi ba.

Yana mayar da martanine ga masu cewa, Tinubu yawa yankin nasu abin azo a gani.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya na barzanar korar ma'aikata, 3,598 daga aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *