In da na ci zaɓe nima sai na cire tallafin man fetur amma ba farar-ɗaya irin na Tinubu ba – Obi

Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, ya ce da ya ci zaɓen da shi ma sai ya cire tallafin man fetur kuma ya kyale Naira ta neman wa kan ta daraja, kamar sai yadda shugaba Bola Tinubu ya yi.
Da ya ke magana a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a jiya Litinin, Obi ya ce da zai aiwatar da manufofin a hankali a hankali ba farar-ɗaya ba gaba-gaɗi irin na Tinubu ba.
Tsohon gwamnan na Anambra ya ce kowa ya san cewa dole ne a kawo karshen “baƙala da cin hanci da rashawa” da ke tattare da tsarin tallafin man fetur.
Obi ya yi tambaya kan inda kudaden da ake tarawa cire daga tallafin man fetur suke tun lokacin da aka cire shi, ya kara da cewa kudaden ya kamata a sanya su wajen yin aiyukan samar da “mahimman kayan more rayuwa”.
Ya ce ba a samu wani gagarumin ci gaba ba tun bayan cire tallafin man fetur.
Ya kara da cewa da zai yi shawarwari da masu gudanar da aiki kan ingantaccen tsarin farashi na samfurin.