
Kasar Uzbekistan sun je gasar cin kofin Duniya a karin farko a tarihinsu.
Duka ‘yan wasan kasar an basu kyautar motoci bayan sun yi nasara akan kasar Qatar a wasan karshe da suka buga.
Gidan Uzbekistan aka je kuma sune suka ci Qatar Kwallaye 3-0.
Bayan kammala wasan, an kawo motocin BYD guda 40 inda aka baiwa kowane dan kwallon kasar makullin sabuwar mota.