Friday, December 5
Shadow

Karanta Jadawalin manyan gurare 7 da aka sakawa sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tun bayan da ya hau mulki

Tun daga 29 ga watan Mayu na shekarar 2023 bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zama shugaban Najeriya, an sakawa manyan gurare na gwamnati guda 7 sunansa.

Daga cikin abubuwan da aka sakawa sunan Shugaban kasar akwai tituna, Barikin sojoji, dakunan taro da sauransu.

Wata kungiyar rajin kare hakkin bil’adama me suna (NEFGAD) ta bayyana hakan a matsayin abinda bai dace ba dan ya sabawa aikin gwamnati.

Ga jadawalin gurare 7 da aka sakawa sunan shugaban kasar kamar haka:

Babban Filin Jirgin sama na jihar Naija.

A ranar March 10, 2024 ne gwamnan jihar Naija, Umar Bago ya sakawa babban filin sauka da tashin jiragen jihar dake Minna sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Karanta Wannan  Sanatocin Jihar Kebbi 3 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Hukumance a zaman majalisa na yau

Titun Abuja Southern Parkway.

A ranar May 28, 2024 ne bayan kammala titin Abuja Southern Parkway, Ministan babban birnin tarayya, Abuja din ya sakawa ritin sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Dakin karatu na majalisar Tarayya

A ranar May 29, 2024 ne majalisar tarayya dake Abuja ta sakawa dakin taro na majalisar sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Dakin Kimiyya da Fasaha na hukumar shige da fici na kasa;

A ranar December 10, 2024 ne hukumar shige da fici ta kasa, Nigerian Immigration ta sakawa sunan dakinta na kimiyya da fasaha sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Kwalejin kimiyya da fasaha dake Gwarimpa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Zai bar Tiktok saboda idan aka rubuta "Sarkin Muni" Tiktok shi suke nunawa

A ranar January 16, 2025 ne gwamnatin tarayya ta amince da kafa kwalejin kimiyya da fasaha a Abuja wadda aka sakawa sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

A ranar January 23, 2025 aka sakawa sabuwar barikin sojoji dake Asokoro sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

A ranar June 10, 2025 ne aka sakawa babban dakin taro na kasa da kasa dake Abuja sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bayan sabuntashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *