
Kasar Iran ta sanar da ficewa daga tattaunawar sulhu kan mallakar makamin kare danginta.
Kafafen yada labarai na kasar Iran din sun tabbatar da hakan inda hakan ke zuwa yayin da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ke gargadin Iran din da ta yadda a ci gaba da tattaunawa ko hare-haren da za’a kai mata nan gaba yafi na yanzu muni.
A ranar Lahadi me zuwane dai ake tsammanin cewa za’a ci gaba da tattaunawar Sulhun amma yanzu Iran tace ta fice daga tattaunawar.
Hakan na iya kara kazanta fadan inda kasar Amurka na iya shigowa cikin fadan.