Tuesday, May 19
Shadow

Tsohon Tsageran Naija Delta, Tampolo yawa shugaban kasa, Tinubu alkawarin kuri’u Miliyan 10 a zaben 2027

Wata kungiya karkashin tsohon tsageran Naija Delta, Tampolo ta yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu alkawarin kuri’u dubu 10 a zaben 2027.

Daya daga cikin shuwagabannin kungiyar me suna Comrade Sunday Adekanbi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar ‘yancin Najeriya a Abuja inda ya jawo hankalin ‘yan Najeriya da su shiga kungiyar.

Yace a shekaru 2 da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi yana Mulki, ya dora Najeriya a Turbar ci gaban tattalin arziki.

Yace zasu yi aiki bisa jagorancin Tampolo dan tattaro kan ‘yan Najeriya su goyi bayan gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarar 2027.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon Da Duminsa:Yanda Matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta kùnyàtà gwamnan jihar Osun yayin da yake tsaka da jawabi tace ta bashi minti 5 ya gama jawabin da yake ya wuce ya ishesu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *