
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, duk wanda baya tare da Gwamnatin Tinubu na iya zuwa ya mutu dama mun yi yawa a Najeriya.
Yace shi zai bayar da filima a binne duk me son mutuwa.
Wike ya bayyana hakane inda yace ya gani a wani gidan talabijin ana sukar sakawa babban dakin taro na Abuja sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Wike yace dalilin da suke bayarwa wai shine me yasa ba’a saka sunan wanda ya gina dakin taron ba.
Wike yace wannan maganar banza ce.
Yace akwai gurare da aka sakawa sunayen manyan mutane wadanda basu ne suka ginasu ba irin su FIlin Jirgin sama n Murtala dake Kano da