
Gwamnatin Tarayya a ranar Juma’a ta bayyana aniyarta ta son tayar da kamfanin Karafa na Ajakuta dan kirkiro ayyukan yi ga matasa.
Gwamnatin tace Tuni ta fara hadaka da kamfanonin kasar China da kuma neman kudi dan tayar da kamfanin da ya dade a lalace.
Hakan na cikin shirin ministan Karafa, Shuaibu Audu wanda a yanzu haka yake jagorantar wata tawaga daga Najeriya zuwa kasar China dan jawo hankalin masu zuba Jari zuwa Najeriya.
Hadimin Ministan, Lizzy Okoji ya bayyana cewa, tuni tawagar ta fara ganawa da kamfanonin kasar China irin su Sino Steel, da Fangda Steel da Jingye Steel.
Ministan yace dawo da kamfanin karafan na Ajakuta ya ci gaba da aiki na daya daga cikin abubuwan da gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta sanya a gaba kuma zasu cimma nasara kamin karshen mulkinsa.