
Ma’aikatar Noma ta Najeriya ta yi kiran da a dauki Azumi a tsakanin ma’aikatan hukumar dan neman Allah ya wadata kasa da Abinci.
Sanarwar hakan na kunshene a cikin sanarwa wadda wakilin ma’aikatar, Adedayo Modupe ya fitar inda yace ana bukatar addu’ar domin taimakawa kokarin Gwamnati na wadata kasa da abinci.
Yace ana tsammanin duka ma’aikatan hukumar zasu fara wannan Azumi dan neman taimakon Allah.
Sanarwar ta bukaci kowane ma’aikacin hukumar ya dauki azumi ranar Litinin ya je dashi wajan aiki.