
Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, FCTA ta sanar da shirin sake gina sabuwar Hukumar zabe me zaman kanta, INEC.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne zai kaddamar da fara ginin na INEC wanda na daga cikin bikin cikarsa shekara 2 akan mulki.
Ba dai a bayyana ainahin nawaye kudin da za’a yi amfani dasu wajan sake gina sabuwar hukumar INEC din ba amma an ce zasu kai Biliyoyin Naira.
Da aka binciki cewa, me yasa FCTA zata gina INEC saboda lura da INEC hukuma ce me zaman kanta, wata majiya daga hukumar ta FCTA tace ai sune suka gina hukumomi da yawa a Abuja hadda ma majalisar tarayya.
Sannan sake ginin bashi da wata alaka da kokarin nuna iko da hukumar ta INEC.