
Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya nemi mutanen Abuja da su daina sauraren karairayin da ake musu a kafafen sada zumunta.
Hakanan yace su daina sauraren ‘yan Adawa wadanda kansu ba a hade yake ba.
Ya bayyana hakane a wajan kaddamar da wani titi a Apo.
Inda yace a baya karairayi kawai ake musu amma a yanzu gashi ana fada da cikawa.
Wike ya jawo hankalinsu da su goyi bayan Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu dan shine ya musu aiki na zahiri.