Friday, December 5
Shadow

An ramawa Kura Aniyarta: Kalli Yanda kasar Ìràn ta mayar da wani sashe na kasar Israyla kamar Gàzà

Shiga Tasharmu ta WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VbA9rBN1SWt61nQZUj1g

Hotunan sakamakon hare-haren da kasar Ìràn ta kaiwa kasar Israyla a jiya na ramuwar gayya na ci gaba da bayyana inda ake ganin yanda makaman Ìràn din suka yi rugu-rugu da gine-gine da dama a kasar ta Israyla.

‘Yan Jarida da yawa sun ce basu taba ganin an yiwa kasar Israyla irin wannan barnar ba a tarihin ta, wasu na cewa gani suke kamar suna Gàzà ne.

Kasar Israyla dai ta mayar da yankin Gàzà kusan kufai inda ra ruguje gidaje da dama.

Karanta Wannan  ABIN A YABA: Malama Hajara Kenan Wacce Ta Gina Katafaren Sabon Masallaci A Unguwar Ndeshi Dake Karamar Hukumar Mokwa A Jihar Neja
https://twitter.com/gizzmo1414/status/1933776593039864163?t=f2OSLdbm4bnjyax4s2a7-w&s=19

Bidiyon ya bayyana inda aka ga wasu Falasdiynawa na murnar hare-haren da Ìràn ke kaiwa kasar Israyla.

https://twitter.com/DD_Geopolitics/status/1933890153266995427?t=dsnK7ZW3RrjwxzIdEJj_nw&s=19

Da yawa musamman wadanda ke goyon bayan Gàzà sun nuna jin dadinsu da ganin abinda Ìran tawa Israylan.

Wasu rahotanni sun ce shugaban kasar Ràshà Vladimir Putin yayi tayin shiga tsakanin kasashen gud biyu da yin sulhu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *