
Shugaban kasar Amurka Donald Trump na shirin dakatar da karin kasashe 36 daga shiga kasar Amurkar kuma ana tsammanin Najeriya ka iya shiga ciki.
A cikin kasashen da Trump din ke shirin dakatarwa akwai kasashen Afrika guda 25 ciki hadda kasar Egypt da Djibouti sannan akwai kasashen Asia.
Kafar the Washington post ta kasar Amurkar tace ta yi kokarin jin ta bakin fadar White House amma abu ya ci tura.