
Babban dan Bindiga, Ado Aliero yace shi da yaransa ba zasu daina kai hare-hare da yin garkuwa da mutane ba sai an daina kiransu da sunan ‘yan ta’adda.
Zagazola Makama ya ruwaito cewa, Aliero ya fadi hakane a Dan Musa jihar Katsina yayin da aka yi zaman Sulhu dasu.
Sarakunan gargajiya, Jami’an tsaro da shuwagabannin kananan hukumomi da ‘yan Bindigar ne suka halarci wannan zaman na sulhu.
Yace da yawan matasa da suka shiga harkar garkuwa da mutane matsin rayuwa nw ya jefasu cikin harkar.
Yace iyayensu basa farin ciki da irin wannan rayuwar da suke yace ko da su kansu a zuciyarsu ba son irin wannan rayuwar suke ba, sun fi so a koma girmama juna musamman tsakaninsu da manoma.
Yace dan haka kamin ma a fara maganar sulhu sai kowane sashe ya girmama dayan sashen.