
Shiga tasharmu ta WhatsApp dan samun labarai: https://whatsapp.com/channel/0029VbA9rBN1SWt61nQZUj1g
Ma’aikatar noma ta Najeriya ta bayyana cewa manyan ma’aikatan hukumar ne ke ta mutuwa shiyasa ma’aikatar ta fito da tsarin yin Azumin dan neman taimakon Allah.
Hakan na zuwane bayan da aka samu rahotanni dake cewa, ma’aikatar ta nemi ma’aikatan ta da su dauki azumi dan neman nasarar wadatar Abinci a Najeriya.
Saidai a sanarwar da mataimakiyar me yada labarai ta hukumar, Ezeaja Ikemefuna ta fitar tace zancen ba haka yake ba.
Tace manyan ma’aikatan hukumar ne ke ta mutuwa akai-akai shiyasa suka fito da tsarin yin addu’a ta hanyar Azumi dan neman sauki da daukin Allah.
Saidai Tuni an dakatar da yin azumin wanda da za’a fara ranar Litinin bayan da cece-kuce yayi yawa akan Lamarin.