
Rahotanni sun ce Kamfanin Multichoice wanda su DSTV suke karkashin sa sun tafka mummunar asara saboda ‘yan Najeriya da yawa sun daina saka kati suna kallon tashoshin.
Kudin shigar kamfanin a shekarar data gabata yayi kasa da kaso 44 cikin 100 inda a yanzu suka samu kudin shiga da ya kai dala Miliyan $197.74.
Saidai a shekarun baya suna samun kudin shiga da ya kai dala Miliyan $355.93.
Hakan na nufin sun tafka asarar dala Miliyan $158.19 idan aka kwatanta da shekarar data gabata.
Lamarin dai bai zowa mutane da mamaki ba musamman ganin yanda kasar ke cikin hali na matsin tattalin arziki.
Hakan kuma baya rasa nasaba da karin kudin subscription da DSTV din suka yi daga Naira N29,500 zuwa Naira 37,000 duk wata.