
Rahotanni daga jihar Jigawa na cewa, Hukumar Ilimin bai daya UBE ta jihar ta dakate da albashin malaman makarantar Firamae 239 da aka samu da laifin rashin shiga aiki su koyar da dalibai ko rashin zuwa wajan aiki.
Shugaban hukumar, Prof. Haruna Musa ya bayyana cewa wannan kokari ne na tsaftace aikin gwamnati.
Sannan yayi kira ga al’umma da su rika lura su kai karar wadanda basa zuwa wajan aikin.
Daga cikin wadanda aka dakatar da albashin nasu akwai malamin da ya shekara 3 kanan bai je wajan aikin ba