Friday, December 5
Shadow

Saudiyya ta ɗauki nauyin kula da alhazan Iran har sai sun samu damar komawa gida

Ma’aikatar Aikin Hajji da Umara ta Saudiyya ta fara shirye-shiryen ganin an bai wa alhazan Iran da ke Makkah da Madinah dukkan kulawa da ta kamata.

Wannan ya biyo umarni da gwamnatin ƙasar ta bayar, na ganin an kula da alhazan ƙasar har sai sun samu damar komawa gida.

Ma’aikatar ta ce jami’anta na aikin duba irin kulawa da ake bai wa mahajjatan Iran 76,000, don tabbatar da cewa babu abin da ya same su yayin da suke Saudiyya.

Haka kuma, ma’aikatar tare da haɗin gwiwar takwararta ta Iran, sun tsara yadda za a yi shirin mayar da alhazan gida.

“Muna son a gudanar da shirin mayar da alhazan na Iran cikin tsanaki ba tare da wata matsala ba,” in ji ma’aikatar ta Aikin Hajji da Umara.

Karanta Wannan  Duk da kisan da akawa mutane a jiharsa, Gwamnan Yobe,Mai Mala Buni yana gidansa dake Abuja bai koma jihar tasa ba

Alhazan za su bi ta filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah da kuma na Mohammed bin Abdulaziz a Madinah, sannan su zarce na birnin Arar, har su kai gida.

An fara aikin jigilar alhazan ne tun ranar Juma’a, inda jami’ai ke ƙoƙari sau da ƙafa wajen ganin an mayar da kowa lami lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *