
Tsohon Ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung ya yi zargin cewa wataran za’a tashi kawai majalisar Dattijai ta mayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shugabab dindindin har iya tsawon rayuwarsa.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a jaridar Sunnews.
Solomon Dalung yace ‘yan majalisar saboda tsabar biyayyar da suke wa shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu idan suka ganshi sai ka ga kamar irin jikoki sun ga kakansu.
Yace irin biyayyar da suke masa ta yi yawa zata sa a rika yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya karan tsaye ba tare sa bin doka ba wajan gudanar da gwamnati.