Friday, December 5
Shadow

Ana zargin “Gwamnan Gombe baya son Shugaba Tinubu yayi takara da Shettima a zaben 2027 saidai Tsoro ya hanashi fitowa ya fada”

Shiga tasharmu ta WhatsApp dan samun labarai: https://whatsapp.com/channel/0029VbA9rBN1SWt61nQZUj1g

A yayin da ake dambarwa kan rade-radin canja mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima kamin zaben shekarar 2027.

Rahotanni daga jaridar Vanguard na cewa, Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa, Gwamnan Gombe, Inuwa Yahya baya son shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ci gaba da tafiya da Kashim Shettima a matsayin mataimaki musamman a zaben shekarar 2027.

Saidai Gwamnan ya kasa fitowa ya fadi abinda ke zuciyarsa saboda tsoro.

Bakan na zuwa ne bayan da aka tashi Baran-Baran a taron masu ruwa da tsaki na Arewa maso gabas saboda an kira sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu amma ba’a kira sunan Kashim Shettima ba.

Karanta Wannan  Mutane Miliyan 1.3 ne suke mutuwa duk shekara saboda shakar hayakin taba duk da su ba mashaya tabar bane

Ana zargin akwai yiyuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai canja Kashim Shettima ya dauko ko dai kirista ko kuma wani musulmin daga Arewa dan ya samu ya sake samun musamman kuri’un ‘yan Arewa a zaben 2027.

A source told Vanguard: “The governor of Gombe State was not in support of the joint ticket, but could not summon the courage to openly oppose it as the host.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *