
Tsohon hadimin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, Aliyu Audu ya bayyana cewa dalilin da yasa ya sauka daga mukamin me baiwa shugaban kasar shawara ta musamman shine yana munafurtar shugaban kasar.
Yace ba zai yiyu ya ci gaba da zama a gwamnatin Tinubu ba bayan yasan cewa, yana kitsa yanda zai fadi zabe a shekarar 2027.
Aliyu ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV inda kuma ya nanata cewa lallai zasu kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027 me zuwa.
A baya dai Aliyu ya aikewa shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu da wasika inda yace yana godiya da damar da ya bashi ta yiwa kasarsa Hidima amma kuma ya ajiye mukamin da ya bashin.
Aliyu shine mutum na 3 da ya ajiye mukaminsa daga gwamnatin shuhaba Tinubu bayan Ajuri Ngilale da Hakeem Baba Ahmad.