
Kungiyar mashaya giya a kasar Ghana sun baiwa gwamnatin kasarsu sati 3 ta sauke farashin giyar ko kuma su tsunduma zanga-zanga.
Kungiyar tace membobinta Miliyan 16.65 dake fadin kasar zasu bazama zanga-zanga muddin Gwamnatin bata rage farashin giyar ba.
Daya daga cikin membobin kungiyar, Moses Obuah ne ya bayyana hakan inda yace darajar kudin Ghana da ake cewa, Cedi ta karu dan haka suma suna kiran a rage musu farashin giyar dan samun saukin rayuwa.
Ya koka da cewa, Abin takaici ne ganin farashin abubuwa da yawa ya ragu amma na giya bai ragu ba.