
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanar da cewa ya dakatar da duk wani aiki da yake zai kai ziyara jihar Benue.
Hakan na zuwane bayan da hare-haren da ake zargin fulani makiyaya da kaiwa suka yi sanadiyyar kisan sama da mutane 100 a jihar ta Benue.
Zanga-zanga ta barke a jihar inda kuma aka kai jami’an tsaro na musamman.
‘Yan Adawa tuni suka fara sukar shugaban kasar saboda zargin rashin nuna kulawa sosai akan lamarin.
shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa zai kai ziyyara jihar Benue ranar Laraba.
Ya fadi hakane a ranar Litinin a lokacin da yake kaddamar da wani shirin ruwa a Abuja.
Ya jawo hankalin mutanen jihar ta Benue da su kai zuciya nesa su rika hakuri da juna.