Friday, December 5
Shadow

Ganyen mangoro da amfaninsa

Ganyen mangoro na da amfani sosai a jikin dam adam.

A wannan rubutu, zamu duba amfanin ganyen Mangoro ga lafiyar dan Adam.

A dunkule, Ganyen Mangoro na maganin ciwon sugar, yana hana fata da jiki saurik tsufa, yana maganin Kumburin jiki, ana kuma amfani dashi wajan magance kuna da aka samu dalilin wuta, da kuma idan abinci baya sarrafuwa a jikin da adam.

Ganyen Mangoro na kuma taimakawa tsawon gashi kuma ana zubashi a ruwan wanka ko a hada shayi dashi saboda yana kara nutsuwa da kawar da damuwa.

Ganyen Mangoro na maganin ciwon gabobi na tsufa.

Ganyen Mangoro na maganin ciwon Ulcer da Gudawa da kukan ciki da sauransu.

Karanta Wannan  Ka dakatar da shirin shigo da kayan abinci daga kasar waje, saboda tabbas farashin kayan abinci zai yi sauki amma mu kuma kasuwancin mu zai lalace>>'Yan kasuwar Najeriya suka roki shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Ganyen Mangoro na maganin cutar Asama.

Ganyen Mangoro na taimakawa wajan hana furfura da wuri da kuma kara tsawon gashi, idan mutum ya kone da wuta, ganyen mangoro na magani, hakanan yana maganin kaikayin fata, ko yanka.

Hakanan ana amfani da ganyen mangoro wajan magance cutar koda da damuwa da sauransu.

Ana amfani dashi wajan maganin kwari.

Yanda ake amfani da ganyen Mangoron.

Ana iya busar dashi a dakashi a rika sha kamar shayi.

Ana kuma iya barbadashi a abinci.

Ana iya markadashi ko mirzashi a danyenshi a rika shafawa a fata dan maganin kunar wuta ko kaikayin fata.

Ana iya zubashi a ruwan wanka.

Ana iya konashi a rika shakar kashi ko a shiga cikin hayakin.

Karanta Wannan  Ƴànbìndìgà masu ikirarin jihadi sun kàshè sojoji takwas a Benin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *