Friday, December 26
Shadow

‘Yan Siyasa na ta canja Jam’iyya amma mabiyansu basa canjawa>>Inji Sanata Ali Ndume

Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa ‘yan siyasa na ta canja sheka amma mabiyansu basa canjawa.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV.

Sanata Ali Ndume yace hadakar ‘yan adawa da ake samu abune me kyau wanda ya kamata ace dama can akwaishi.

Yace shekararsa 65 kuma ya shafe sama da shekaru 20 a cikin siyasa dan haka babu abinda ke gabansa yansu sai fadar gaskiya komai dacinsa.

Sanata Ali Ndume ya yi wasu kalamai dake nuna alamun cewa, yana shirin canja jam’iyya.

Karanta Wannan  Shekara ɗaya maƙiya Kano su ka yi su na cin dunduniyar gwamnatin Abba, Cewa Kwankwaso

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *