Friday, December 5
Shadow

Mutane Miliyan 1.3 ne suke mutuwa duk shekara saboda shakar hayakin taba duk da su ba mashaya tabar bane

Rahotan hukumar lafiya ta Duniya, WHO yace mutane Miliyan 1.3 ne ke mutuwa duk shekara daga shakar hayakin taba sigari duk da su ba mashaya tabar bane.

WHO ta fitar da rahoton ne bayan taronta a Birnin Dublin.

Rahoton yace akwai bukatar a samar da tsari da zai dakatar da irin wannan asara da ake yi.

Hukumar ta fito da wani tsari me suna MPOWER wanda tace idan aka bishi za’a samu saukin mutuwar mutane dalilin shan taba Sigari.

Tsarin na dauke da kula da masu shan taba sigari da kuma tsaftace iska da kuma taimakawa masu shan tabar su daina sha.

Karanta Wannan  Matar Rarara, A'ishatulhumaira ta aikawa Baana sammace inda tace ya mata Qazafin yin mu'amala da maza ciki hadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *