
Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP, Kayode Egbetokun ya bayyana cewa, ‘yansanda basa kama mutum dan kawai ya zagi ko sukar dan siyasa.
Yace koshi ana zaginshi a kafafen sada zumunta amma hakan baya sawa a kama mutane.
Ya bayyana hakane ranar Talata a wajan wani taron da aka gudanar a Abuja inda yace amma inda za’a iya kama mutum shine idan ya wallafa labaran karya.
Yace ko da ba akan dan siyasa ba idan mutum ya wallafa labaran karya za’a iya hukuntashi.