
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2027, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa zaben 2027 ba zai zama kamar sauran zabukan da aka yi a baya ba.
Yace ‘yan adawa na hadaka ta musamman dan ganin sun yi nasara akan gwamnati me ci saboda tsare-tsaren gwamnatin basu kawowa kasar ci gaba ba.
Ya bayyana hakane a Abuja ranar Talata a yayin ziyarar da wasu ‘yan masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood suka kai masa.
Kungiyar tace tana tare da Atiku a zabe me zuwa.
Wani dan siyasa daga jihar Zamfara, Dr. Aslam Aliyu ne yawa kungiyar jagora zuwa wajan Atiku.