
Rahotanni sun bayyana cewa darajar Naira ta dan farfado a kasuwar Chanji inda aka rika sayen dala akan Naira 1595 ranar Talata.
Idan aka kwatanta da farashin dalar na naira 1600 da aka rika saye a ranar Litinin, za’a iya cewa darajar Nairar ta karu da Naira 5.
Saidai farashin nairar a kasuwar Gwamnati shine ana sayen dala akan Naira 1550.