Friday, December 5
Shadow

Rikici ya kunno kai a jam’iyyar su El-Rufai ta SDP an dakatar da shugaban jam’iyyar saboda zargin satar kudin jam’iyyar

Jam’iyyar SDP ta sanar da dakatar da shugabanta, Shehu Gabam bisa zargin aikata ba daidai ba da wasu kudaden jam’iyyar.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Araba Aiyenigba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata inda yace bayan shugaban SDP din, an kuma dakatar da me binciken gudanar kudi na jam’iyyar, Nnadi Clarkson, da kuma shugaban matasa na jam’iyyar, Chukwuma Uchechukwu.

Yace kudaden da ake zarginsu da cinyewa sun hada da na siyen fom din takara a zaben 2023 kuma kudaden Miliyoyin Naira ne.

Yace an saka mataimakin shugaban jam’iyyar, Sadiq Abubaka a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na riko.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu zai halarci taron ci gaban Kasashe a Abu Dhabi

Yace kuma sun sanar da hukumar zabe da dukkan hukumomin da suka kamata game da dakatarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *