
Hukumar ‘yansandan Najeriya ta nuna rashin jin dadinta game da abinda wasu jami’anta suka aikata na yiwa jarumar fina-finan kudu, Angela Okorie rakiya yayin da take sanye da shigar banza take gudu.
Bidiyon nata ya watsu sosai a kafafen sada sumunta wanda hakan ya jawo cece-kuce.
Dan haka hukumar ‘yansandan ta fitar da sanarwar cewa abinda ‘yansandan suka aikata baya cikin tsarin aikin dansanda.
Hukumar tace tana kan Bincike kuma zata dauki matakin da ya dace bayan kammala binciken lamarin.