
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan sababbin dokokin haraji huɗu a wani mataki na sauya fasalin tsarin karɓa da tattara haraji na ƙasar.
Gwamnatin ta ce sabbin dokokin za su sauƙaƙa tsarin, da rage wahalhalun haraji kan ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni, da kuma taimakawa wajen inganta karɓar haraji.
“Sauye-sauyen za su taimaki masu ƙaramin ƙarfi tare da tallafa wa ma’aikata ta hanyar ƙara yawan abin da suke samu,” kamar yadda Shugaba Tinubu ya bayyana a watan da ya gabata lokacin bikin cika shekara biyu a kan mulki.
Ya ƙara da cewa: “Sauye-sauyen sun cire muhimmman abubuwa kamar abinci da ilimi da kula da lafiya daga tsarin biyan harajin VAT. Haka nan, sabon tsarin ya keɓe karɓar rance da sufuri da makamashin da ba ya gurɓata muhalli, duka wadannan ba za su biya harajin VAT ba, kuma duk wannan an yi ne domin sauƙaƙa wa magidanta”.
Waɗanne ne sabbin dokokin?
Sabbin dokokokin harajin huɗu da Tinubu ya sanya wa hannu a yau sun haɗa da:
- Dokar haraji ta Najeriya (The Nigeria Tax Act), wadda ta tattara ƙananan tanade-tanaden haraji wuri guda, za ta kawo ƙarshen ƙananan tanadin haraji fiye da 50 a ƙasar. A cikin wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar ta ce rage yawan tanade-tanaden harajin masu cin karo da juna a wasu lokuta, zai ƙara sauƙaƙa harkokin kasuwanci a ƙasar
- Dokar gudanar da haraji (The Tax Administration Act), wadda ta tsara dokokin bai ɗaya na yadda za a karɓi haraji a matakan gwamnatin tarayya da na jihohi da ƙananan hukumomi
- Dokar kafa hukumar karɓar haraji (The Nigeria Revenue Service Act), wadda za ta maye gurbin hukumar karɓa da tattara haraji ta ƙasar (FIRS) kuma wadda aka bayayna da ”mai zaman kanta”, an sanya mata sunan ”Nigeria Revenue Service (NRS)
- Dokar samar da hukumar haɗin gwiwa ta haraji (The Joint Revenue Board Act), wadda za ta inganta haɗin kai tsakanin matakan gwamnati da kula da harkokin haraji da samar da kotun kula da shari’o’in da suka shafi haraji
Gwamnatin ta ce duka waɗanan sabbin dokoki za su taimaka wajen inganta tare da sauƙaƙa tsarin haraji a fadin ƙasar.
Ana sa ran masu ƙaramin ƙarfi, da masu ƙananan kamfanoni, da masu ƙananan sana’o’i, za su fi amfana da waɗannan dokokin.
Ga mutanen da ke samun naira miliyan ɗaya a shekara, za su samu sauƙi na biyan kuɗin haya 200,000, ta yadda kuɗinsu da za a ɗauki haraji ciki zai koma naira 800,000. Hakan zai sa ba za su shiga rukunin masu biyan haraji ba, kamar yadda Andersen Nigeria, wani kamfani mai ba da shawara kan haraji da kasuwanci ya bayyana.
Muhimman ayyuka da manyan abubuwan buƙatu, kamar abinci da kiwon lafiya da biyan haya da wutar lantarki da kayayyakin jarirai, an keɓe su daaga biyan harajin VAT, lamarin da zai taimaki iyalai da dama wajen samun muhimman abubuwan buƙatun rayuwa.
Ƙananan kamfanonin da ke juya ƙasa da naira miliyan 50 a shekara ba za su biya harajin da kamfanoni ke biya ba, kuma ba za a buƙaci su cire kuɗin haraji daga masu sari ba.
Haka nan, za a ba su izinin shigar da abin da suka karɓa zuwa asusun gwamnati ba tare da buƙatar asusunsu domin tantancewa ba.
Manyan kamfanoni za su amfana daga rushewar da aka yi wa ƙananan tanade-tanaden haraji, lamarin da zai sa su samu sauƙi daga kashi 30 zuwa 27 cikin 100 a shekarar 2025 sanna kashi 25 cikin 100 a shekara mai zuwa.
Har ila yau, yanzu za su iya karɓar kuɗin haraji na VAT da aka biya a kan cinikayya da kadarori, ma’ana za su iya dawo da kashi 7.5% da za a biya a matsayin VAT.
Haka kuma sabbin dokokin sun tanadi sauƙin haraji ga ƙungiyoyin agaji, da gidauniyoyin da ƙungiyoyin ilimi da na addini, muddin ba na kasuwanci ba ne.
Wa sabbin dokokin za su fi shafa?
Masu ƙaramin ƙarfi ne kan gaba cikin waɗanda za su fi amfana da sabbin dokokin, mafi yawansu dokokin sun cire su daga biyan haraji, yayin da za su samu sauƙi da rahusa kan muhimman abubuwan more rayuwa.
Alal misali ga iyalin da ke kashe mafi yawan kudinsa kan biyan haya da abinci da sufuri za su ga sauƙi saboda rahsin biyar harajin VAT.
Masu ƙananan sana’o’i su ma za su samu gagarumin sauƙi bayan rushe wasu ƙananan tanade-tanaden harajin da a baya ke taƙura musu.
Hakan zai taimaka musu wajen inganta kasuwancinsu ta hanyar komawa tsarin kasuwanci a hukumance.
Su kuma mutanen da ke samun kudi da yawa da masu amfani da kayyakin ƙawa ko na alfarma, za su ji ba daɗi, saboda ƙaruwar harajin VAT da ake sa ran gani kan manyan kayayyakin ƙawa da wasu ayyukan muhimmai da kuma ƙarin haraji da aka yi kan manyan hannayen jari.
Me ya sa Tinubu ya ce ana buƙatar dokokin?
Gwamnatin Najeriya ta ce tsarin harajin da ƙasar ke amfani da shi ya zama tsohon yayi, wanda ba ya aiki yadda ya kamata, tare da ɗora wa takalawa wahalhalu.
ƙiyasin harajin Najeriya dangane da arzikin da ƙasar ke samu a cikin gida (GDP), babban ma’aunin harajin da ƙasa ke karɓa la’akari da tattalin arzikinta bai fi kasi 10 cikin 100 ba, ƙasa da matsakaicin adadi na kashi 16-18 cikin 100 da ake karɓa a Afirka.
Gwamnatin Tinubu na son ƙara adadin zuwa kashi 18 cikin 100 nan da shekarar 2026 ba tare da ƙara haraji kan muhimman abubuwan buƙatun rayuwa ba, ko ɗora wa masu ƙaramin ƙarfi wahala ba.
Gwamnatin dai na sa ran waɗannan sabbin dokokin za su inganta kuɗin harajin da gwamnati ke samu domin samar da ayyukan more rayuwa a faɗin ƙasar don rage yawan dogaro da bashi da ƙasar ke yi.