Rahotanni daga kasar Rasha na cewa, kasar na takurawa ‘yan Afrika dake kasar shiga aikin soji dan yin yaki da kasar Ukraine.
Rahoton jaridar Bloomberg ya bayyana cewa, kasar ta Rasha tana kuma takurawa hadda dalibai dake karatu a kasar.
Saidai duk da haka wasu na baiwa jami’an tsaro cin hanci dan su kyalesu su zauna a kasar ba tare da su shiga aikin sojan ba ko kuma an dawo dasu gida ba.
Yakin Rasha da Ukraine dai kullun sai kara kazancewa yake inda Ukraine din ke ci gaba da samun goyon bayan kasashen Yamma da Amurka.