Da Ɗumi-Ɗumi
Matar tsohon gwamnan jihar Kebbi Dr. Zainab Shinkafi Bagudu ta sanar da ɗaukar nauyin duk wata waƙa da za a samu wanda zai yi a matsayin martani ga wadda mawaƙi Ali Jita ya yi ta “Uwargida”.

Dr. Zainab wadda ita ce amarya ga tsaron gwamnan wanda a yanzu shi ne Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙin Najeriya, a wani saƙo cikin raha da ta wallafa a shafinta na Instagram ta ambaci sunayen Naziru Sarkin Waƙa, Hamisu Breaker, Auta Waziri, Dauda Kahutu Rarara, Namenj, Ɗan Musa, Umar M. Sheriff da Nura M. Inuwa, ta na mai neman da a samu ɗaya daga cikinsu ya yi musu (su amare) wannan waƙar a matsayin martani.
Cikin waɗannan mawaƙa wa ku ke ganin zai wakar martani da za ta doke wadda Ali Jita ya yi?