Friday, December 5
Shadow

An yiwa Alkalan Najeriya 10 ritayar dole bayan samunsu da rage shekaru dan ci gaba da aiki

Majalisar koli dake kula da harkar Alkalai ta Najeriya, NJC ta yiwa Alkalai 10 daga jihar Imo ritayar dole bayan samunsu da laifukan rage shekaru.

Majalisar ta dauki wannan mataki ne bayan zaman da ta yi bisa jagorancin babbar Alkaliyar Najeriya, Justice Kudirat Kekere-Ekun.

Sanarwar da majalisar ta fitar ranar Alhamis tace akwai alkalai 5 a babbar kotu da alkalai 4 a kotun Customary da aka samu da rage shekaru dan su ci gaba da aiki.

Alkalan babbar kotun da aka cire sune M.E. Nwagboso, B.C. Iheka, K.A. Leaweanya, Chinyere Ngozi Okereke, da Innocent Chidi Ibeawuchi. 

Daga kotun Customary kuma alkalan da aka cire sune, Tennyson Nze, Uchenna Ofoha, Everyman Eleanya, da Rosemond Ibe.

Karanta Wannan  Shugaban kasar Korea ta Arewa ya aikewa da matashin shugaban kasar Burkina Faso, Ibrahim Traore da sojoji su bashi kariya bayan da aka yi yunkurin hambarar dashi

Sannan An yiwa Wani alkali me suna Justice T.N. Nzeukwu ritaya saboda bayyana kansa a matsayin alkalin alkalan jihar Imo duk da matsayinsa bai kai ba.

Majalisar ta ce Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma ya nada alkali mafi girman mukami a jihar a matsayin alkalin alkalan jihar na riko.

Sannan majalisar ta wanke Wani alkali me suna Justice V.U. Okorie, daga cikin masu laifin.

Majalisar ta kuma amince da nadin alkalai daban-daban a jihohin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *