Friday, December 5
Shadow

Fada ya kare tsakanin mu, mun shirya>>Wike da Fubara bayan da Shugaba Tinubu ya sasantasu

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa a yanzu babu sauran rashin jituwa tsakanisa da dakataccen gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara.

Ya bayyana hakane bayan ganawar da suka yi da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da daren ranar Alhamis.

Wike yace komai ya wuce.

Shima Fubara ya bayyana cewa zaman lafiya ya dawo jihar Rivers inda ya bayyana jin dadinsa da ganin wannan rana da suka yi sulhu shi da Wike.

Karanta Wannan  An yi kiran Gwamnatin tarayya ta kama Rotimi Amaechi saboda kiran da ya yiwa talakawa cewa su daina yadda 'yan siyasa da basu wuce mutane Dubu 100 ba na sace dukiyar Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *