
Rahotanni sun bayyana cewa an nada mataimakin shugaban APC na yankin Arewa, Ali Bukar Dalori dan ya maye gurbin Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar na riko.
Hakan na zuwane yayin da aka kira taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar da zai tattauna dan nemo mafita bayan Saukar Ganduje.
Ganduje ya mika takardar barin aiki inda yace yayi hakan ne saboda ya samu damar kula da lafiyarsa.