Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: “Akwai yiyuwar Kwankwaso ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC”

Wani jigo a jam’iyyar APC da bai so a bayyana sunansa ba ya bayyana cewa, akwai alamu masu karfi dake nuna cewa, tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso zai koma jam’iyyar.

A hirarsa da jaridar Guardian ya bayyana cewa, bayan komawar Kwankwaso APC akwai kuma yiyuwar zai zama shugaban jam’iyyar.

Hakan na zuwane kwana daya bayan da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga mukamin shugaban jam’iyyar APC.

Dan APC din ya bayyana cewa, matsawa Ganduje akayi ya sauka daga kan kujerar tasa ba dan yana so ba.

Da aka tambayeshi ko saukar Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC zai iya sa Tinubu ya rasa kuri’ar Kano, sai yace hakan ba lallai ya faru ba domin duk da sauke Ganduje daga mukaminsa har yanzu yanawa uwar jam’iyyar APC biyayya.

Karanta Wannan  Majalisar Jihar Kano ta mayar da Yaren Hausa a matsayin wanda za'a rika amfani dashi wajan koyar da dalibai a makarantun Firamare da karamar Sakandare

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *