
Rahotanni sun ce tursasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje aka yi ya sauka daga shugabancin jam’iyyar APC ba dan yana so ba.
Daily Trust ta ruwaito cewa daya daga cikin shuwagabannin tsaron Najeriya ne ya je har gida ya bukaci Ganduje da ya sauka daga shugabancin jam’iyyar APC.
Wani na kusa da Ganduje yace sun kadu sosai da abinda ya faru.
Saidai a takardar ajiye aiki da Ganduje ya aikewa jam’iyyar APC, yace ya sauka ne dan mayar da hankali wajan kula da lafiyarsa.
Rahoton yace wani gwamna daga Arewa maso gabas da wani daga Arewa sun je yiwa Ganduje jaje.
Ana rade-radin cewa, An cire Ganduje daga shugabancin jam’iyyar APC ne dan kokarin kawo ‘yan siyasa irin su Dr. Rabiu Musa Kwankwaso cikin jam’iyyar.