Ana jan hankalin Namiji ta hanyoyi da yawa.
Budurwa zata iya jan hankalin Namiji ta wadannan hanyoyin:
Kashe murya, Kashe Murya na da matukar tasiri a zuciyar namiji, muddin zaki kashe muryarki wajan yiwa Namiji magana, zuciyarsa zata yi sanyi.
Fari Da Ido: Eh! Yin fari da ido amma ba na rashin kunya ba, yana jan hankalin namiji shima yaji har cikin zuciyarsa ta motsa.
Shagwaba: Shagwaba na sa Namiji yaji yana sonki sosai, musamman kina yi kina masa magana irin ta ‘yan yara.
Kwalliya: Kwalliya na jan hankalin Namiji sosai, Kisa kaya masu haske da daukar ido wanda da ya ganki zai ji yana son sake kallo.
Turare: Turare na jan hankalin Namiji, ko da bai yi niyyar mayar da hankali kanki ba, turarenki zai iya jan ra’yinsa.