
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi jimamin rasuwar Aminu Dogo Dantata a sakon da ya fitar ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga.
Shugaban yace wannan rashi ne da Najeriya ta yi baki daya.
Yace za’a tuna Dantata da kasuwancin da yayi da kuma taimakawa da yayi wajan hadin kan Najeriya ta wajan bayar da tallafin da ya amfani mutane da yawa.
Tinubu ya bayyana Dantata a matsayin mutumin da ya bashi gudummawa wajan shawara me kyau.
A karshe ya mikawa iyalan mamacin sakon ta’aziyya.