Friday, December 5
Shadow

An kama wasu ‘yan kasar China 14 a Najeriya bisa aikata miyagin Laifuka za’a mayar dasu kasarsu, Ji laifukan dansuka aikata

Babbar kotun tarayya dake da zama a Ikoyi jihar Legas ta daure wasu ‘yan kasar China 14 da aka kama bisa zargin aikata damfarar yanar gizo da taimakawa ‘yan ta’adda.

Hukumar EFCC tace ta kama su ne a wani samame data kai a cikin birnin legas din a watan December 19, 2024.

EFCC tace ‘yan Chinar na daga cikin mutane 792 data kama kuma an gurfanar dasu a gaban mai shari’a Justice Daniel Osiagor.

Da farko sun ki amsa laifukan nasu amma daga baya sun amsa cewa sun aikata laifukan.

Lauyoyin EFCC, T.J. Banjo da M.S. Owede sun nemi kotu ta daure wadanda ake zargin kuma lauyoyin wadanda ake zargin basu nemi kada a yi hakan ba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Gwamna Zulum ya tarar da ma'aikatan gidan Gwamnati dake zuwa aiki da wuri ya basu kyautar Naira Miliyan 2 kowannen su

A karshe an yanke musu hukuncin daurin shekara daya a gidan yari ko kuma biyan tarar Naira miliyan daya sannan da zarar sun gama zaman gidan yarin ko biyan tarar an nemi a mayar dasu kasarsu China.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *